Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa Bataliyar Sojoji da kuma Rundunar ‘Yan sanda a Karamar Hukumar Birnin Gwari cikin Jihar Kaduna.
Wannan amincewa ta na daya daga cikin matakan da gwamnatin za ta dauka domin gaggauta magance harin kashe-kashe da ke yawaita a jihar.
Kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a jiya Litinin da dare.
A jiya Litinin din ne kuma Sarkin Birnin Gwari ya ce yawan wadanda mahara suka kashe a shekaranjiya ya kai mutane 58 a wani hari guda daya da suka kai a kauyen Gwaska.
A baya ma an sha kashe sojoji da ‘yan sanda a hare-haren dajin Birnin Gwari.
Garba Shehu ya kuma bayyana takaici da jimamin Buhari dangane da kashe-kashen inda ya ce ya nuna damuwar sa matuka, kuma ran sa ya sosu. Ya na kuma taya iyalan mamatan jimami da damuwa.
Shehu ya ce wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka na kafa bataliyar sojoji da rundunar ‘yan sanda a yankin, sabon yinkuri ne na ganin an shawo kan yawan asarar dukiyoyi da rayuka da ake yi a Benuwai, Zamfara, Kaduna, Taraba da Nassarawa.
Sai dai kuma duk da kafa sojoji da aka yi a Benuwai da Taraba, har yanzu ana ci gaba da kashe-kashe babu kakkautawa a wasu daidaikun yankunan jihohin biyu.
Ya ce samar da tsaro na daga cikin shiri mafi muhimmanci ga wannan gwamnati, don haka ba za a lamunci wasu tsiraru da ke haddasa fitina wajen cusa kiyayya ga ‘yan Najeriya ba.
“Wadannan kashe-kashe na da alaka da masu wata boyayyar mafuna da ke haddasa fitintinun gaba tsakanin al’ummomin kasar nan da nufinn kitsa barkewar yaki don su kuma su cimma ta su manufar.”
El-Rufai ya ziyarci Birnin Gwari
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya kai ziyara a garin Gwaska, inda mahara suka kashe kimanin mutane 58.
Gwamnan ya kuma gana da Sarkin Birnin Gwari, Jibril Zubair da sauran shugabannin yankunan al’umma kafin ya karasa Gwaska, inda aka yi mummunan kisan.
A fadar Sarkin, El-Rufai ya nuna matukar bakin ciki kuma ya yi wa iyalan wadanda aka kashe ta’aziyya.
Ya tabbatar musu da cewa abin ya na matukar damun sa da kuma gwamnatin sa, amma da iznin Allah ya zu magance wannan harin ta’addanci da al’ummar yankin Birnin Gwari ke fama da shi.
Shi kuma Sarki Jibril Zubair, ya yaba da ganin yadda gwamnati ta kamo hanyar shawo kan matsalar gadan-gadan.
Ya na mai cewa a matsayin sa na daya daga cikin mambobin majalisar tsaro ta jihar Kaduna, ya san irin namijin kokarin da ake a kai yanzu domin magance hare-haren.
A garin Gwaska, wani dagaci mai suna Isa Musa ya zagaya da gwamnan kuma ya ba shi labarin yadda abin ya faru.
“Sun shigo mana dauke da manyan makamai, kuma ba kananan mahara ba ne. Sun kutso ta ko’ina suka kewaye mu su na harbi su na banka wa gidajen mu wuta.
“Mu na godiya da kokarin da ku ke yi, amma fa maganar gaskiya magance wannan matsala fa sai dai zaratan sojoji na kasa da kuma na sama kawai. Rikakkun mahara ne mutanen da ke kashe mu. Domin ai tsakanin mu da Dansadau bai fi kilomita bakwai ba. Ga kuma kan iyakokin Katsina da Nijar duk a nan Birnin Gwari.”