ABIN DA BA KU SANI BA: Yajin aikin ma’aikatan Jinya da na Lafiya dake karkashin kungiyar JOHESU, Daga Khadijatu Muhammad

0

A gaskiya ya kamata mu sanar wa mutanen Najeriya da duniya baki daya cewa mambobin kungiyar JOHESU ba su saba doka ba sannan fara yajin aiki da suka yi ba laifin su bane ko kadan suna haka ne domin su kwato wa kan su hakkin su.

Idan har akwai wadanda za a tuhuma ko ayi wa korafi kan matsalolin da ake fuskanta a dalilin wannan yajin aiki, ba zai wuce gwamnatin Najeriya ba da ma’aikatar kiwon lafiya karkashin shugabancin Ministan Kiwon Lafiya, Isaac Adewole.

Ita dai Kungiyar JOHESU ta kunshi, ma’aikatan kiwon lafiya a asibitoci, da suka hada da kwararru kan abinda da ya shafi magani, daukar hoto, masu duba hakora, wato likitocin hakora, masu kula da dakunan shan magani da na allura, dakunanna ajiye kayan aiki, masu kula da marasa lafiya da yi musu hidima, masu yin inkiya zuwa ga likitoci da sauran ma’aikatan asibiti duk a karkashin kunyar JOHESU su ke.

Mutane basu da masaniya game da menene ainihin kukan mu da abin da muke bukata gwamnati tayi mana. Ya kamata mai karatu ya gane cewa lallai amfanin mu na da yawa kuma kamar ma kusan mune asibiti idan babu mu babu asibiti.

GA BUKATUN MU NA GASKIYA WANDA AN YI WA LIKITOCIN SUMA

1 – A gyara mana albashi kamar yadda aka gyara wa likitoci a shekarar 2014, wanda likitan da ya kammmala NYSC wato bautar kasa ake fara biyan sa albashi daga naira dubu dari uku da goma 310,000 amma pharmacist wato wanda ya kware kan harkar magani, da wasun su ake biyan su naira 118,000 kacal, Ina adalci a ana?

Bayan mu ne ke kwana awowi 24 da mara lafiya mu zo aiki da wuri daga 8 na safe mafi yawan lokuta likita ba zai zo aiki ba sai waje karfe 11 na safe hakan zai sa marasa lafiya suyi ta zaman jiran sa, ba komai ke hana su zuwa da wuri ba illa ziyartar asibitocin su na kudi wanda yin hakan karya dokar kasa da dokar aikin gwamnati ne.

Likita basu aiki a kauyuka wanda acewar sabon Shugaban kungiyar likitoci wai rayuwar kauye bata kamace su ba. Mune ke aikin a asibitocin kauyuka, mu kwana mu uni wurin sadaukar da rayukan mu na yi wa kasa aiki.

Duk da zunzurutun kudin da suke kwasa a asibiti gwamnati da na kudi bai ishe su ba namu ne ya tsole musu ido suna ikirarin tsunduma ya jin aiki indan gwamnati ta amsa bukatun mu.

2 – Idan dai gwamnati na so ta yi adalci baza ta ce likita ne kawai zai ke rike madafun iko ba a asibitocin ta da ma’aikatar lafiya ta kasa da na jaha domin a kasashen duniya mafi yawan hukumomi ba likitoci bane ke sama a wuraren nan ana ba kowa gashin kan sa tare da adalci.

3 – Muna so mu zama kwararru (consultants) akan aikin mu wanda ko me aikin zane-zane yana zama kwararre wanda a kasashen duniya ma muna zama amma likitocin Najeriya sunce indai gwamnati ta yardar mana zasu fara yajin aiki.

4 – Tunda likitoci suke yajin aiki ba’a taba rike musu albashi ba amma mu an rike mana duk da mun yi aikin kwana 18 a a watan Afrilu.

Suna kin zuwa aiki wanda idan kaje wajen su sai su ce ka dawa bayan yajin aiki ya kare daga nan sai su karakata ka zuwa asibitocin su na kansu, wanda suna nan da yawan da zasu iya yin mafi yawan aikin da taimakon daliban su.

Duk wanda ya saurayi hirar RAAYI RIGA NA BBC HAUSA zai ji yanda masu jinya suka koka kan irin wulakanci da rashin tausayi da suke musu sannan su sallame su.

Duk wannan adawar da suke mana mafi yawanci su iyayen su daga cikin mune nurses wasu sun auri mafi yawan mambobin JOHESU amma bai hana su hassada da kyashi damu ba.

Kuma sabo da tsabar kiyayya da mugunta irin na likitoci da ministan lafiya suke fadawa duniya wai ahalin yanzu mambobin JOHESU na kai musu farmaki da barazana wanda karya ce kawai.

Likitoci ne ke danne mu, suke muzguna mana sannan suke nuna ko ta halin kaka sai sun cimma burin su na ganin ma’aikatan lafiya ba su samu nasa a abin da suka sa a agaba ba

ina kira kira ga mambobin JOHESU su dage da addu’a sannan su sani mu gwamnati muke wa yajin aiki ba wani can likita ba duk surutan da suke yi kan mu, mu tsoshe kunnuwar daga jin su har sai mun cimma burin mu, kuma rashin albashi na dan lokaci ne amma idan ba mu daure ba zaluncin su na har abada ne.

Sannan Muna kira ga ‘yan Najeriya musamman marasa lafiya da su yi mana afuwa, da zaran mun cimma ma tsaya tsakanin mu da gwamnati zamu dawo bakin aiki sannan kuma kira ga gwamnati da mai girma shugaba kasa yayi mana adalci ya fidda mu daga kangin azzaluman likitocin nan!!!

Share.

game da Author