A sanarwar da shugaban kungiyar JOHESU Biobelemoye Josiah, ya fitar da yammacin Alhamis, ya yi kira ga ma’aikatan asibitocin kasar nan da suke yajin aiki da su koma bakin aiki.
Biobelemoye ya ce kungiyar ta amince ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da tayi da sauran mambobin ta da kuma bin umarnin kotu.
Ya ce duk da janye yajin aikin za a ci gaba da tattaunawa da jami’an gwamnati domin ganin an biya musu bukatun su.
Kungiyar ma’aikatan asibitocin kasar nan sun shiga yajin aiki ne sama da kwanaki 40, suna neman gwamnati ta biya musu wasu muhimman bukatun su.
Hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin su da makarraban gwamnati har ma da likitocin kasar nan da suke ganin bai kamata ace wai sun shiga yajin aiki tun da farko.