Mutan Kaduna sun kwankwadi romon dimokradiyya – Abdullahi

0

Kwamishinan kasafin Kudi da tsare-tsare na jihar Kaduna Mohammed Abdullahi ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta kashe sama da naira biliyan 152 don yin manya-manyan ayyuka 1,053 a fadin jihar.

Abdullahi ya ce karamar hukumar Zariya ce ta fi ko wace karamar hukuma a jihar samun ayyukan raya gari inda gwamnati ta kashe naira biliyan 55 wa manyan ayyuka 99.

Bayan haka Kwamishina Abdullahi yabawa gwamnan jihar Nasir El-Rufai, kan nasarorin da jihar ta samu a tsawon shekaru uku na mulkin Kaduna.

Yace gwamnati ta kashe naira biliyan 113 wajen yin wasu manyan ayyuka a jihar, inda ayyukan raya jihar kawai ya lashe naira biliyan 85, fannin ilimi akayi mata kason naira biliyan 20, kiwon lafiya kuma ta kwankwadi naira biliyan 5.

Cikin nasarorin da aka samu zuwa yanzu sun hada da gyara makarantu da gina sabbi 700 da kuma daukar kwararrun malamai 25,000.

“A fannin kiwon lafiya gwamnati ta gina sannan ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya sama da 160 duk da akwai saura da za a kammala nan da karshen wannan shekara.

“Bayan haka gwamnati ta gyara hanyoyi masu yawa a fadin jihar.

Ya ce gwamnati ta maida hankali wajen samar wa mutanen jihar ababen more rayu, bayan kokarin kafa kamfanoni da take yi a jihar, Kamar su Kamfanin Olam, kamfanin taraktoci da kamfanin samar da wutanlantarki na sola da dai saura su.

Share.

game da Author