‘Yan fashi sun sace albashin ma’aikatan karamar hukumar Gwandu, jihar Kebbi

0

Shugakan karamar hukumar Gwandu jihar Kebbi, Shehu Bagudu ya sanar cewa wasu ‘yan fashi sun waske da kudin albashin ma’aikatan karamar hukumar.

Barayin sun tare kashiyan karamar hukumar ne bayan ya jido kudin daga banki zai kai gida a motar sa, suka kwashe kudin ta-tas bayan kuma jira kawai ake gari ya waye a biya ma’aikata albashi.

Bagudu yace an tsinto motar kashiyan a karamar hukumar Tambuwal jihar Sokoto.

Bayan haka Bagudu ya karya ta jita jitan da ake ta yada wa cewa wai shi Bagudun na kare kashiyan daga binciken jami’an tsaro saboda sirikin sa ne.

” Gwandu siriki na ne tun kafin na zama shugaban karamar hukuma sannan ko da ya sami aiki a karamar hukumar Gwandu kowa ya na mishi shaidar mutumin kirki ne.

A karshe jami’in harka da jama’a na rundunar ‘yan sandar jihar Mustapha Suleiman ya tabbatar da faruwar wannan abin takaici sannanan bada belin Kashiyan dake tsare.

Bayani sun nuna cewa ‘yan uwa da iyalen kashiyan na kokarin ganin sun biya wadannan kudade kafin a shigar da kara kotu.

Share.

game da Author