Sanata Dino Melaye ya caccaki shugaba Buhari a Majalisa

0

Sanata Dino Melaye ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari, in da ya soki bayanan da yayi cewa babu wani abin azo a gani da ‘yan majalisun suka tabuka banda zaman dumama kujera da suke yi.

Buhari ya ce wasun su sun fi shekara 10 a majalisar, amma babu abin da suka tabuka.

Dino Melaye da ya tashi a zauren majalisar yau, a fusace ya nuna bacin ran sa ga wadannan kalamai da shugaba Buhari yayi yana mai cewa, katobara ce fadin haka sannan tozartar da majalisar ne.

Bayan haka Sanata Dino ya mika faifai dake dauke da maganganun shugaba Buhari kan abin da yace game majalisar.

A karshe Dino ya ce abinda Buhari ya fadi babu dattaku a ciki sannan ya saba wa doka.

” A dalilin haka ina kira da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya aiko da neman afuwar sa ga duka ‘yan majalisar, ya roki mu mu yafe masa.

Share.

game da Author