Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a cikin shekaru uku na mulkin sa an samu karuwar hasken lantarki, a gefe daya kuma garin san a asali, Daura da ke jihar Katsina ya shafe kwanaki 10 babu hasken lantarki.
A yayin da ya ke karanta jawabin bas a a ranar Dimokradiyya, Daura da sauran garuruwan da ke kewaye da garin duk babu wutar lantarki, sakamakon rugujewar wani sabon babban turken wayoyin samar da wuta mai karfin hasken lantarki har 132kva.
Cibiyar dai ba a dade da kafa ta ba, kuma an yi kirdadon cewa za ta shekara 30 ba tare da samun wata tangarda ba.
Sai dai kuma ba a dade da bude ta ba sai wani iska mai karfi da ya zo tare da ruwan sama ya tumbuke shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon kakakin majalisar jihar Katsina Umar Gwajo-gwajo ya koka cewa rashin wutar ya jefa al’ummar shiyyar da Daura da kewayen ta a jikin kunci musamman a lokacin azumin nan, kasancewa kuma ana fama da matsanancin zafi.
Kakakin Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano, wato KEDCO mai suna Mohammed Kandi, ya bayyana cewa tuni an tura ma’aikata, su na kokarin shawo kan matsalar.
Da ya ke tattaunawa da PREMIUM TIMES ta waya, Kandi ya ce wasu turakun wayar kuma har 16 duk sun fadi sakamakon wannan iska mai karfi da aka yi.
Amma ya tabbatar da cewa nan da awa 48 za a kammala komai, kuma za a maida wutar a yankin na Daura.