Jega ya fito ya fallasa Sanatocin da ya ce su na karbar cin hanci – Majalisa

0

Majalisar Dattawa ta kalubalanci Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC) Attahiru Jega, da ya fito ya fallasa sanatocin da ya ce kwararru ne wajen neman cin hanci a wajen shugabannin hukumomin gwamnati.

Wannan kiran ya biyo bayan korafin da Sanata Isa Misau daga jihar Bauchi ya yi, inda ya nuna bacin ran sa da kalaman da Attahiru Jega ya yi na zargin cewa sanatoci, musamman shugabannin kwamitoci sun kware kwarai wajen tambayar cin hanci daga shugabannin hukumomi.

Jega ya ce shugabnnin jami’o’i sun sha kai masa wannan korafin ba sau daya ba, ba sau biyu ba.

Sanata Misau ya ce babban abin damuwa dangane da zargin da Jega ya yi wa Majalisar Dattawa shi ne, an haska jawabin na sa a talbijin, duk duniya ta kalla, kuma ta saurare shi.

Da ya ke maida martani, Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ce shi ma din Jega ya bata masa rai, kuma bai ji dadin abin da ya fada ba, musamman saboda ya na a wurin ne ya yi wannan furucin.

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zanta ta Kasa, Attahiru Jega, ya bayyana cewa mambobin Majalisar Tarayya rikakkun kwararru ne wajen neman a ba su cin hanci da rashawa kafin su gudanar da ayyukan da dokar kasa ta wajabta musu su aiwatar.

Attahiru Jega

Da ya ke jawabi a wurin laccar Tunawa da Ranar Dimokradiyya, a Cibiyar Taro ta ‘International Conference Center’ a Abuja, ranar Litinin, ya ji daga bakin da dama daga cikin manyan shugabannin hukumomin gwamnati, sun yi masa korafin yadda mambobin Majalisar Tarayya ke yawan neman a ba su cin hanci kafin su biya wa hukumomi bukatun da doka ta wajabta a biya musu.

Farfesa Jega, ya shaida wa dimbin mahalarta taro, ciki har da Shugaba Muhammdu Buhari, Yakubu Dogara, Babban Alkalin Alkalai na Kasa, Walter Onnoghen cewa “wasu Shugabannin Kwamitocin Majalisar Tarayya basu kware da iya komai ba, sai neman a ba su cin hanci kafin su yi wa hukumomin gwamnatin tarayya abin da ya wajaba su yi musu.”

Wannan bayani da Jega ya yi, ya kara tabbatar da rahoton da PREMIUM TIMES ta yi kwanan baya cewa shugabannin hukumomin gwamnati na koken cewa mambobin majalisar tarayya na uzura musu da neman a ba su toshiyar baki kafin su amince da wata bukata ta su.

Share.

game da Author