Kotu ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari

0

Idan ba a manta ba, babbar kotu dake Abuja ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame da laifin wawushe kudin jihar da ya kai naira biliyan 1.6 a lokacin da yake gwamna.

Nyame yayi gwamna a jihar Taraba ne daga 1999 zuwa 2007.

A zaman kotun a Abuja ranar Laraba, Alkali Adebukola Bankole ya bayyana cewa irin yadda Nyame da makarraben sa suka saci kudaden da yadda akayi ta dibar su gunduwa gunduwa, yayi kama da labarin kasurgumin barawon nan mai suna Ali Baba da Barayin sa arba’in.

Wani da ya ba da shaida a kotun yace tun farko dai an fara satar ne da dibar miliyan 345 daga asusun gwamnati inda aka saka a asusun wani kamfani mai Saman global.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun yace Nyame ya amsa laifuka 21 ciki 47 da ake tuhumar sa a kai. A dalilin haka kotu ta yanke masa zaman kurkuku har na tsawon shekaru 14, babu tara.

Nyame zai garzaya gidan maza ne kai tsaye ko kuma ya daukaka kara.

Share.

game da Author