Dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Kachia da Kagarko, jihar Kaduna, Hon. Adams Jagaba, ya fice daga jam’iyyar APC, ya koma PDP.
A yau ne Shugaban Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya karanta takardar da Jagaba ya rubuta wa majalisa a matsayin sanarwar sa ta yin canjin sheka zuwa PDP.
A hira da yayi a Kaduna a kwanakin baya, Jagaba ya ambata tun a wancan lokacin cewa ya fice daga APC sai dai bai fadi jam’iyyar da zai koma ba.
” Jam’iyyar APC ta zama kwale-kwalen da ke tangal-tangal a cikin ruwa. Ni dai ba zan tsaya har ya nutse da ni a ciki ba.” Inji Jagaba.