A yau Laraba ne Sanatan da ke wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye ya bayyana wa ‘yan uwan sa sanatoci a zauren majalisa cewa, zai canza wurin zama daga bangaren ‘yan APC zuwa bangaren ‘yan jam’iyyar adawa, wato PDP.
Dino da yau ne ranar sa ta farko da ya halarci zaman majalisar, tun bayan kamawar da ‘yan sanda suka yi masa, makonnin da suka gabata.
Ya shafe tsawon kwanaki a gadon asibiti, tun bayan dirowar da ya yi daga motar ‘yan sanda a Abuja.
Da ya ke jawabi a Majalisar Dattawa a yau Laraba, ya gode wa Mambobin Majalisar Dattawa da na Tarayya da kuma ‘yan mazabar sa da sauran ‘yan Najeriya, wadanda ya ce sun tsaya bayan sa a lokacin da ya shiga cikin halin tsaka-mai-yawa.
Daga nan kuma ya gode wa shugabannin jam’iyyar PDP da ya ce sun tsaya bayan sa.
Melaye, wanda ya je Majalisar daure da bandejin da ya tallabe wuyan sa, ya nemi Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da ya umarci Dogarin Majalisa ya samar masa wurin zama a bangaren ‘yan adawa.
Daga nan sai ya ce zai zauna a bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, kafin a samar masa wurin da zai rika zama na dindindin.
Nan da nan sai wasu daga cikin sanatoci suka taimaka masa, suka karasa da shi wurin zaman da ya zaba din.
Sai dai kuma har yanzu a shari’ance bai kai ga zama dan jam’iyyar PDP ba, tukunna. Har sai ya rubuta wa Shugaban Majalisar Dattawa wasikar sanar da shi tukunna.
Daga nan sai a karanta wasikar a gaban majalisa.