Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan wasan kwallon kafa ta Kasa Super Eagles, a safiyar Laraba.
Wannan dai ziyara ce na yi wa shugaba Buhari sallama a shirin su na tafiya kasar Rasha domin fafatawa a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a fara ranar 14 ga wannan wata na Juni.
Kafin nan, Super Eagles din za su buga wasar sada zumunta da kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila ranar Asabar mai zuwa.