Ya Ku ’Yan Najeriya!
A yau Dimoradiyyar mu ke cika shekaru 19 da sake kafuwa da kafafun ta, kuma shekara uku da kama mulkin da muka yi. Wannan gwamnati ta zo a daidai lokacin da ake bukatar canji, kuma wannan canjin muka yi alkawarin tabbatarwa. Mun fuskanci kalubale wajen tabbatar da samar da abubuwa uku da muka yi alkwari, wato Tsaro, Kawar Da Cin Hanci, sai Inganta Tattalin Arziki.
2. Muna murnar wannan rana ta yau a matsayin ranar bikin jaddada ‘yanci a karkashin gwamnatin da ta jajairce kai ‘yan Najeriya ga tudun-mun-tsira karkashin shimfida adalci da samar da yalwa.
3. Inganta tsaron rayukan jama’a shi ne ginshikin wannan gwamnati. Domin an ga yadda muka yi kokarin dakushe Boko Haram a cikin shekaru uku.
4. An ceto daliban Chibok 106, na Dapchi 104 sannan an ceto wasu sama da 16,000 daga hannun Boko Haram.
5. An kafa sansanonin gudun hijira wadanda aka inganta da kayan kula da lafiya da abinci da sauran kayan bukatu na yau da kullum.
6. Ana ci gaba da kokarin maida masu gudun hijira a garuruwan su, tare da kafa musu makarantu, asibitoci, samar musu da ruwa da sauran abubuwan bukatu.
7. Ana kuma kokarin kawo karshen mummunan kashe-kashen da ya addabi kasar nan da kuma matsalar yawaitar garkuwa da mutane.
8.Ina godiya ga sojojinn hadin-guiwa daga Chadi, Nijar, Benin da Kamaru da kuma na mu na nan gida Najeriya a kokarin su na yaki da ta’addanci a Arewa maso gabas.
9. Wannan gwamnatin ta damu kwarai da irin yawan asarar rayukan da Boko Haram suka haddasa da ma sauran rikici a kasar nan.
10. An samu zaman lafiya sasai a yankin Neja Delta ta hanyar janyo dattawan yankin da sauran masu ruwa da tsaki da gwamnati ta yi wajen shawo kan matsalar yankin.
11. Babban kudirin wannan gwamnatin na biyu shi ne ta kashe cin hanci da rashawa a kasar nan, tun kafin cin hanci da rashawa ya kashe kasar.
12. An shigo da tsare-tsare domin toshe hanyoyin da ake cin hanci da wawurar kudade, kuma hakar mu na cimma ruwa sosai.
Akwai hanyar Asusun Ajiyar Bai-daya.
Kwarmaton-hura-usur.
Gano ma’aikatan bogi 52,000.
13. An kwato biliyoyin nairori ta hanyar amfani da EFCC ana bin diddigin wadanda suka saci dukiyar kasar nan.
14. Mun kulla yarjejeniya da kasashe da dama wajen kokarin gano inda wadanda suka saci kudade suka kimshe dukiyoyin su a kasashe daban-daban. Hakan ya na nufin babu inda mutun zai iya guduwa ya boye bayan ya wawuri kudin kasar nan.
15. Wannan gwamnati ta maida hankali wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan da ta gada a daidai lokacin da ya ke shure-shuren mutuwa.
16. An gida kakkarfan ginshikin tattalin arziki tare da tare da yi masa ingantaccen kandagarkin da har ya na ci gaba da farfadowa, kamar yadda kididdiga ta nuna a kowace shekara.
17. A yau asusun ajiyar mu na waje ya na da dala bilyan 47.5, amma a shekarar 2015 dala bilyan 29.6 ne kacal.
18. Ana ci gaba da inganta ayyukan noma, sufuri, sarrafa kayayyaki da kuma harken lantarki da iskar gas.
19. Najeriya na cigaba da samar da wadataccen abinci na cikin gida wanda zai wadace mu, har mu daina dogaro da komai daga kasashen waje.
20. Tsarin inganta rayuwar jama’a ta hanyar samun jarin dogaro da kai ya na samun tagomashi sosai.
Ana ci gaba da aikin ciyar da dalibai a jihohi 24, inda aka dauki masu aikin dafa abinci har 75,000, su na ciyar da dalibai milyan 8.2.
Ana ci gaba ra raba tallafinn naira 5,000 ga masu karamin karfi a wasu jihohin kasar nan. Nan gaba shirin sai baibaye kaf jihohin kasar nan har da Abuja.
An ga yadda tsarin N-Power ke samar wa matasa aiki. An dauki 200,000 kuma har an zabi wasu 300,000 daban da wadancan.
22. Mun kara samun karfin hasken lantarki har miga wats 5,222.3. Yanzu karfin lantarki ya haura miga wats 7,500.
23. Ana kokarin a ga cewa hasken lantarkin ya kai ga duk wanda ke bukata a cikin farashin da ba a tsauwala ba.
24. Fannin sufuri ma ya samu kyakkyawar kulawa, tun daga filayen girgin sama zuwa titinan fadin kasar nan da kuma bangaren jiragen kasa.
26. An samu gagarimin ci gaba sosai a cikin shekara uku din nan wajen inganta manya da kananan titinan kasar nan a kowace shiyya.
27. Sannan an ga kokarin da muke kan yi wajen inganta fannin zirga-zirgar sufirin jiragen kasa.
28. A fannin ilmi gwamnati ta amince za ta kafa Kwalejin Tarayya, kuma ta bada lasisin kafa jami’ar jiha hudu da kuma manyan kwalejojin fasaha masu zaman kan su 14, sai jami’o’i masu zaman kan su 12.
29. Duk sauran bangarorin ilmi a kowane mataki ana ba shi kulawar da ta kamata, tun daga tsarin UBE da sauran hukumomi da cibiyoyin ilmi duk an kashe musu makudan kudade wajen ingata su.
30. Har yanzu gwamnati ta na ceto jihohi daga halin kaka-ni-ka-yi ta hanyar tallafa musu da kudaden ceton ran su da aka fi sani da ‘bailout.’ Domin ta haka ne kawai za su iya samu su rika biyan albashi da alawus-alawus.
31. Cikin wadannan shekaru uku an yi ayyukan kandagarkin kwararowar Hamada har guda 73 a jihohi daban-daban, kuma yanzu haka akwai wasu ayyukan har 53 da ake kan kaddamarwa a fara.
32. Ba mu manta da gudummawar da matan kasar nan suka bayar ba a cikin shekaru uku wajen kokarin ganin an inganta Najeriya. Muna alfahari da ku a matsayin ku na iyayen mu kuma iyayen kasar mu.
33. Ina rokon ‘yan Najeriya mu cire kiyayyar juna da ta yi mana katutu a zukata, ta haka ne kawai za mu iya zama cikin lumana da wanzuwa a cikin salama.
34. Ga zabe ya gabato, kowa ya taimaka wajen tabbatar da cewa an gudanar da zabe lami lafiya a cikin kwanciyar hankali. Kuma a yi zabe sahihi, ingattace ba tare an yi tashe-tashen hankula ba.
35. Kwanan nan zan sa wa dokar da za ta bai wa matasa damar shiga a dama da su a cikin mulkin kasar nan hannu.
36. Ina godiya da zaman sauraren jawabi na.
37. Allah ya albarkaci Najeriya.
Discussion about this post