Mazauna unguwannin Fadaman Mada, Gida Dubu, Awalah da kwatas din Madina sun koka kan yadda ‘yan achaba da ke aiki a wadannan yankuna suka addabi mutane da sare-sare a jihar.
Mutanen wadannan unguwanni sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa haka kawai sai kaga mutum ya dumfaro ka akan babur da sharbebiyar makami tsirara, kafin ka ankara ya daba ma ya yi tafiyar sa.
Bayanai sun nuna cewa wadannan unguwanin sun yi watanni biyu suna fama da wannan matsalar.
” Tsakanin wadannan watanni biyu ‘yan achaban sun kai sassari mutane 10. iya wadanda za mu iya kirga wa inda cikin su biyu sun rasu.
Daya daga cikin wadanda suka sha daga hannu irin wadannan mutane Isiaka Hamisu dake zama a kwatas din Madina ya bayyana cewa ‘yan achaba sun daba masa makami haka kawai ranar lahadin da ta wuce.
” Ina tafiyata zuwa gidana da misalin karfe takwas na dare sai kawai naji an sare ni da makami an gudu. Karshen ta dai sai da aka akaini asibiti aka duba ni.
Shima Husaini Umar dake zama a Fadaman Mada yace ‘yan achaban sun sare shi ne ranar Alhamis a hanyar sa na zuwa gida da karfe 7:30 na yamma.
Limamai da shugabannin unguwannin da wannan ta’addancin yayi kamari sun yi kira ga gwamnati da ta mai da hankali wajen ganin ta tsaurara matakan tsaro a fadin jihar.
Sun koka kan yadda irin wannan salon ta’addanci ya addabi mutanen jihar.
A karshe kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi Kamal Abubakar ya ce sun kama mutane 12 da suke zargi da aikata hakan.
Kamal yace duk sun kama wadannan matasa ne da makamai a jikin su.