Wani gungun ‘yan Najeriya sun gudanar da zanga-zangar neman a cire shugabannin hukumomin sojojin kasar nan, su na cewa ba su da wani amfani, domin sun kasa magance mummunan kashe-kashe da ake ta yi, ba kakkautawa a kasar nan.
Gungun masu zanga-zangar dai sun fito daga bangarori daban-daban daga fadin kasar nan, inda suka tattaru a Dandalin Unity Fountain da ke Abuja, suka yi zaman da suka kira Zaman Makokin asarar dimbin rayukan da ake yi a fadin kasar nan.
Wanda ya hada zanga-zangar mai suna Chidi Odinkalu, ya ce babban makasudin fitowa su yi zanga-zangar shi ne kawai a cire dukkan shugabannin fannonin tsaron kasar nan, tunda ba su da wani amfani, a sauya su da wadanda za su iya magance bala’in da Najeriya ke ciki.
Tun daga ranar 1 Ga Janairu, jihohin Benuwai, Kaduna, Taraba, Zamfara, Adamawa da Edo ke cikin rikicin kashe-kashe, kuma har yau babu alamun kawo karshen matsalar.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bi diddigin wata mahawara da aka yi a gidan Talbijin na Channels, tsakanin Tsohuwar Ministan Ilmi, Obey Ezekwelise, Junaid Mohammed da kuma Festus Keyamo, sabon daraktan yada labarai na kamfen din zangon shugaba Muhammadu Buhari na biyu a zaben 2019.
A cikin mahawarar da aka tafka, Junaid Mohammed ya nemi a cire dukkan shugabannin hukumomin tsaron kasar nan, saboda sun kasa tabuka komai wajen kawo karshen kashe-kashen da ake yi.
Wadanda masu zanga-zanga ke neman a cire sun hada da Hafsan Sojojin Kasa, Tukar Buratai, na Sama, na Ruwa, da Babban Hafsan Tsaro, Ministan Tsaro, Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Shugaban Hukumar Leken Asiri da kuma Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro.
Har ila yau kuma su na so a cire Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau.
Ministan Tsaro, Mansir Dan’Ali dai dan Jihar Zamfara ne, jihar da aka fi kashe-kashe a fadin kasar nan.
Discussion about this post