Kungiyar likitoci na ‘Society for Family Physicians of Nigeria (SOFPON)’ da kamfanin ‘Sevenz Healthcare’ sun kirkiro shafi na yanar gizo mai suna ‘Komplete Care’ da zai taimaka wajen rage yawan lokacin da ake batawa wurin jiran ganin likita da marasa lafiya ke yi a asibitocin kasar nan.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Akwa Ibom Dominic Ukpong ya sanar da haka a taron kungiyar SOFPON wanda aka yi a watan Mayu a babbar asibitin koyarwa dake Uyo (UUTH).
Ukpong ya bayyana cewa za a iya samun wannan shafi ne a yanar gizo wato a ‘Google play’.
‘‘Bayan likita da mara lafiya sun yi rajista a wannan shafi,marasa lafiya za su iya ganawa da likitan da suke bukata sannan shi likitan zai iya bada magani,ya ce a yi gwaji da sauran su bayan ya saurari mara lafiya
” Wannan shafi ta samar wa marasa lafiya damar ganawa da kowani likitan da za su bukata ta wayan tarho ko Komfuta batare da sun je asibiti ba.”
A karshe wata ma’aikaciyar asibitin ‘Emmanuel Hospital’ dake Eket Nene Andem ta jinjina kan kirkiro wannan shafi.
Ta ce idan dai za a yi amfani da wannan fasaha zai taimaka wajen rage wahalolin da marasa lafiya kan yi fama da su a asibiti.
Discussion about this post