A yau Litinin ne hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Zamfara Mahmood Aliyu Shinkafi, da tsohon ministan kudi Bashir Yuguda, Aminu Nahuche, da Ibrahim Malaha.
Gaba dayan su ana zargin su ne da hannu dumu-dumu wajen amsar kudin kamfen din 2015 daga rumbun kudaden da tsohuwar ministan Mai na Kasa, Diezan Madueke ta yi ta raba wa.
Kudin da ke tuhumar Shinkafi da handame wa sun kai naira miliyan 450 tare da sauran wadanda ake zargin na su tare.
Yanzu dai a halin da ake cike an basu beli, ciki da ya hada da kowa ya mika hoton fasfo dinsa na kwana-kwanannan da kuma fasfo din tafiyar sa sannan da belin naira miliyan biyar da wasu mutane biyu da zasu tsaya maka.
Za a ci gaba da sauraren karar ne ranar 27 da 28 din watan Yuni.