PREMIUM TIMES ta samu kwafen rahoton bayanin da EFCC ta yi dangane da zargin wawurar kudade da aka yi wa Olusegun Obasanjo.
Sa-toka-sa-katsi ta yi zafi bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zargin Dala biliyan 16 ta salwanta da sunan gyara ko inganta wutar lantarki, amma babu wani takamaiman abu da za a iya nunawa an yi da duka kudden.
Nan da nan Obasanjo ya maida martani ya nuna cewa Buhari ya jahilci batun aikin wutar lartakin da aka gudanar a zamanin sa can shekarun baya.
PREMIUM TIMES ta samu kwafen rahoton da Darakta a EFCC na Lokacin, Ibrahim Lamurde ya sa wa hannu.
ZARGIN DA AKA YI WA OBASANJO
Gwamnan Jihar Abia ne na lokacin, ya rubuta wa EFCC takardar zargin Obasanjo ya wawuri kudade.
Orji Uzor Kalu ya rubuta takardar ne a ranar 22 Ga Augusta, 2005 ya aike wa EFCC.
ZARGI NA BIYU KAN OBASANJO
Shi kuma wata kungiya ce mai yaki da shugabannin da suka waruri kudade mai suna C.A.C ta yi shi a karkashin shugaban ta Debo Adeniran, a cikin Nuwamba, 2007.
Ita kuma wannan takardar korafin ta kunshi zarge-zargen cewa an hada baki da wasu sanatoci da mukarraban Obasanjo, aka wawuri kudaden fetur da na kwangilar harkokin tsaro.
Akwai kuma zargin amfani da naira biliyan 40 aka gina makarantar Obasanjo mai suna Bells Secondary School da Unibasiti. An ce kamfanin gini na Strabag ne ya yi masa aikin ginin.
An kara zargin Obasanjo da harkallar kudin mai fetur a matsayin sa na Ministan Man Fetur a lokacin da ya ke shugaban kasa tsakanin 1999 zuwa 2006.
An yi zargin Obasanjo ya karkatar da wasu kudade naira bilyan 6.5 daga cikin kudaden da aka tara masa domin gina dakin karatu.
Sai harkallar gonar sa Obasanjo Farms wadda aka ce ya inganta ta da kudaden gwamnati, wacce a lokacin da ya ke tsare a kurkuku, gonar kusan ta zama kufai. Amma sai ga shi bayan ya zama shugaban kasa ta zama ita kadai ce ke shigo da abincin kaji daga waje.
Zargin yin aringizon kasafin 2005 aka kara naira biliyan 133, sai kuma aka zurara naira bilyan 521 a fannin inganta hasken lartarki, amma ba a samu lantarkin ba.
Sai zargin karkatar da naira miliyan 200 ya sayi hannun jari a Transcorp, ya kashe kudin kasa wajen yinkurin yin Tazarce, sai kuma kashe naira bilyan 300 kan aikin titina, alhali ba a ga wani gyaran a zo a gani a kan titinan ba.
BINCIKEN DA EFCC TA YI
Hukumar EFCC ta ce bayan ta karbi korafe-korafen, ta tura tawagar bincike a makarar Bells ta Obasanjo, Gonar Obasanjo da kuma Kamfanin Strabag da kuma wurin jami’an Dakin Karatun Obasanjo.
An kuma tura wa Orji Uzor Kalu wasika domin ya sadu da jami’an bincike, yadda zai taimaka musu da fito da kwararan hujjoji ba ji-ta-ji-ta ba.
An kuma rika bin Urji Uzor Kalu da yawan kiran wayar sa a nan Najeriya da kasashen waje, domin neman karin haske, tunda shi ne ya rubuto korafin zargin.
“Kai har bugawa a jaridu EFCC ta yi cewa ta na rokon Kalu ya tuntubi EFCC domin ya bada damar a same shi a ji karin bayani da hadin kan sa yadda za a fito da hujjojin daga cikin zargin da ya yi wa Obasanjo, amma Kalu ya yi kunnen-uwar-shegu da EFCC bai je ya bayar da goyon bayan yin binciken zargin da ya yi ba.
“Amma shi wanda ya yi zargi na biyu, wato Debo Adeniran, ya amsa gayyatar neman karin haske da EFCC ta yi masa.” Inji EFCC din.
PREMIUM TIMRES ta tuntubi Debo kuma tabbatar mata cewa tabbas ya rubuta wa EFCC korafi a cikin Nuwamba, 2007 akan Obasanjo, kuma ya kai a ofishin ta na Lagos.
Daga nan ne shugabar EFCC ta lokacin, Farida Waziri ta kafa kwamitin bincike, karkashin Ibrahim Lamurde.
“Tabbas an gayyace ni na je, amma daga nan kwamitin bincike bai sake gayyata ta ba. Ko bayan da Obasanjo ya kare kan sa, ba a sake kira na na maida masa raddi ba.” Inji Adedeiran.
YADDA OBASANJO YA KARE KAN SA
Shi dai Obasanjo ya musanta dukkan zarge-zargen da Kalu da Adedeji suka yi masa, y ace bait soma kan sa cikin kowace harkalla a lokacin da ya n shuagaban kasa ba.
Ya ce gonar sa dai kowa ya sani tun cikin 1979 ya kafa ta bayan da ya sauka daga shugabancin kasa na mulkin soja. Sai kuma ya ci gaba da inganta ta a cikin 1995, kuma a lokacin ana samun gagarimar riba, kafin a daure shi a kurkuku, inda daga nan kuma gonar maimakon riba, sai faduwa aka rika fuskanta.
Obasanjo ya ce amma cikin 1998, kamar yadda rahoton ya nuna, sai aka farfado da gonar, ta rika samun gagarimar ribar da tilas ta sa aka kara fadada gonar sosai.”
Dangane da makarantar sa Bells kuma, ya ce an fara gini cikin 1995 ta hanyar aikin lebura na ci-da-karfi, wato ‘direct labour’, wanda shi da kan sa ne ke zama ya na duba yadda ake yin ginin.
Dangane da zargin harkallar man fetur kuwa, Obasanjo ya ce ai akwai Ma’aikatar Man Fetur da kuma Babban Daraktan NNPC na lokacin, su ne ke da alhakin bayar da kwangiloli, kuma su ya kamata a fara tuntuba domin neman bayani.
Obasanjo ya ce bai taba mallakar katin Musamman na Cirar Kudade da ake kira Platinum Credit Card ba, a duk tsawon rayuwar sa.
Sannan ya ce bai taba mallakar asusun ajiya a kowace kasa ba. Ya kuma kira EFCC da ta baza komar ta a kowace kasar duniyar nan domin ta bincika ta gani.
Game da kwangilar harkokin tsaro kuma, ya ce Ma’aikatar Tsaro ya kamata a je a bincika a tabbatar, ba a tsaya ana rara-gefe ba.
ABIN DA EFCC TA GANO
EFCC ta binciki takardun kwangiloli da rasidan biyan kudin kwangilolin Hukumar Tsaro, amma babu inda sunan Obasanjo ya fito.
Makarantar Bells ta fara da gini biyu a 1991, zuwa 1998 an kara gina ajujuwa biyu na maza da mata.
Bincike ya tabbatar da cewa aikin ci-da-karfi ne leburori suka yi, ba kamfanin Strabag ne ya gina ajujuwan ba kamar yadda aka yi korafi a a cikin zargin.
Bincike ya tabbatar da cewa Strabag bai taba aikin kwangilar gini ko da na aza bulo daya a gonar Obasanjo ba.
Dukkan kwangilolin fetur da aka ce an bayar, babu inda ko da a wuri daya sunan Obasanjo ko na wani kamfani na sa ya fito.
An tara wa Dakin KARATUN Obasanjo naira biliyan 3.5 da kuma dala 250,000. Daga cikin kudade, an biya kamfanin kwangila, Messrs Gitto Construction Company naira bilyan 1.3, da sauran kananan ‘yan kwangila da masu tuntubar binciken aikin gini.
Ranar 26 Ga Mayu, 1999, kwanaki uku kafin a rantsar da Obasanjo, ya kulla yarjejenya a wani kamfanin lauyoyi mai suna Lucky Egede and Daniel Atsu, domin su karbi ragamar gudanar da harkokin gonar sa, wato Ota Farms, shi kuma ya tsame hannun sa.
An kuma cire sunan Obasanjo daga cikin jerin sunayen daraktocin gonar duk a cikin 1999.
An soke yarjejeniyar da Obasanjo ya yi da kamfanin lauyoyin bayan ya sauka daga shugabancin kasar nan a cikin 2007.
An gano Obasanjo ramto kudi ya yi a cikin 1998 a bankin First Bank da Unioun Bank har naira milyan 40 domin ya inganta gonar sa. Ya ramto kudin cikin 1998, kafin ya zama shugaban kasa.
Binciken na EFCC ya bayyana cewa tsakanin 1999 zuwa 2007, Hukumar Lantarki PHCN ta karbi naira bilyan 273.5 kacal daga gwamnati, ba naira biliyan 521.
Dukkan kwangilolin da PHCN ta bayar binciken takardu da rasidai sun tabbatar da babu inda sunan Obasanjo ko na wani dan uwan sa ya fito ya karbi kwangila.
Lokacin da aka fara binciken zargin kashe kudi a shirin tasarce, EFCC ta buga tanda cewa duk mai wata shaida da za ta iya nuna cewa Obasanjo ya kwashi kudi ya yi kamfen ba tazarce, to ya fito ya kai mata, amma ba a samu hujja ko da guda daya ba.
“Dangane da wannan bincike da EFCC ta yi, babu ta inda za a iya kafa wata ko wasu hujjojin cewa akwai hannun Obasanjo.