Jam’iyya mai mulki APC da mai adawa, PDP sun mika jadawalin lissafin adadin kudaden da kowace ta ce ta kashe a zaben 2015.
Adadin ya nuna cewa gaba dayan su biyu din bas u kashe abin da ya kai naira bilyan 8 ba.
Yayin da APC ta ce ka kashe naira bilyan 2.9, ita kuma PDP ta bayyana cewa naira bilyan 4.8 ta kashe.
Dukkan dalla-dallan bayanan su na cikin rahotannin da kowa daga cikin jam’iyyun biyu suka damka wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Kasa, INEC.
Kamar dai yadda dokar kasa ta tanadar, kowace jam’iyya sai ta mika wa INEC rahoton kudaden da ta kashe a wajen yakin neman zabe.
Sannan kuma dokar ta ce INEC ita kuma za ta buga jadawalin da kowace jam’iyya ta samu a cikin akalla jaridun kasar nan uku.
Sai dai kuma maimakon a ce kowace jam’iyya ta gabatar da na ta rahoton ga INEC lokaci kadan bayan kammala zaben shugaban kasa, dukkan su biyu sun kawo rahoton na su a makare, bayan shekaru uku da yin zabe.
Tunda gwamnati ta daina daukar nauyin jam’iyyun siyasa cikin 2010, su kuma sai suka daina tura wa gwamnatin rahoton kudaden da suke kashewa, kamar yadda aka umarce su da su rika yi.
Jam’iyyu sun yi tankiyar cewa tunda dai gwamnati ta daina daukar nauyin su, to babu dalilin da zai sa kuma su rika bayyana mata abin da su kuma suke kashewa wajen daukar dawainiyar jam’iyya da kuma yakin neman zabe.
Discussion about this post