Ba za mu bi umarnin kotu ba na mu janye yajin aiki – JOHESU

0

Kungiyar ma’aikatan asibitoci da na jinya da ke karkashin kungiyar JOHESU, ta bayyana cewa ba za su bi umarnin kotu ba na su janye yajin aikin da suka fara tun a watan Afrilu.

Shugaban kungiyar ya ce ba za su janye yajin aiki ba duk da wannan umarni na kotu domin kuwa sun riga sun shigar da kara tuntuni na rashin cancantar wannan kotun ‘Indutrial’ ta saurari karar da gwamnatin tarayya ta shigar na a tilas ta musu su koma aiki.

Shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya gana da ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewole da na kwadago Chris Ngige, gami da shugabannin Kungiyar ma’aikatan jinya da na asibitocin kasar nan domin tattauna yadda za a kawo karshen yajin aikin da JOHESU suka shiga tun a watan Afrilu.

Saraki ya ce za su ci gaba da tattauna wa da JOHESU da ministocin had sai an daidaita.

Idan ba a manta ba ana nan ana ta kai ruwa rana tsakanin kungiyar JOHESU da gwamnatin tarayya, inda ita kungiya ke neman lallai sai a inganta wa ma’aikatan asibiti albashi da sauran alawus-alawus kamar yadda likitoci ke morewa a kasar nan.

Hakan dai ya durkusar da ayyukan asibitocin kasar nan inda kullum kara tabarbarewa ya ke yi.

Gwamnati sun kasa gano bakin zaren.

Share.

game da Author