Gwamnatin Buhari bin ‘yan adawa take tana bugewa kamar kaji

0

Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana cewa a halin da kasar nan ta samu kanta yanzu, babu sauran abinda ya rage ace ana mulkin kama karya.

Wike ya ce maimakon gwamnati ta maida hankali wajen inganta rayuka da walwalan mutanen Najeriya, karkatawa ta yi zuwa farautar ‘yan adawa.

” Ya kamata Buhari ya kwaikwayi yadda salon mulkin Jonathan yake a wancan lokaci, na inda bai muzguna wa ‘yan adawa ba, sannan baya bi yana bigewa kamar kaji, irin yadda wannan gwamnati take yi.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kakkabe katunan zaben su, su shirya tuge wannan gwamnatin da ya kira na yaudara a kasa Najeriya.

Gwamna Wike yayi wannan tsokaci ne a taron kaddamar wani katafaren Sabon ofishin gwamnan Jihar Ekiti, da akayi bukin haka a garin Ado-Ekiti.

Bayan haka kuma Wike ya nanata cewa ana nan ana ta yi masa bita da kulli, ana farautar ran sa. ” Wannan gwamnati na son su ga baya na, rai na suke farauta.

Jiga-jigan jam’iyyar PDP da ya hada da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, gwamnan Gombe Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, Shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, Gwamnan Jihar AkwaIbom, Delta da wasu jiga-jigan jam’iyyar ne suka halarci bukin.

Share.

game da Author