EFCC ta tsare Ramalan Yero na awa 4 a ofishin ta

0

A safiyar yau Juma’a ne tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero ya bayyana a hukumar EFCC dake titin Wurno, Kaduna.

Tsohon gwamna Yero ya shafe awa hudu a ofishin EFCC ya na amsa tambayoyi daga hukumar.

Yero ya isa ofishin da misalin karfe 9 na safe ne amma bai fice daga hukumar ba sai da karfe 1: 30 na rana.

Fitowar sa ke da wuya sai ya iske dandazon magoya baya a gaban ofishin suna jiran sa.

” Nagode da nuna mini kauna da kuka yi. Yanzu kuma sai duk mu tafi masallacin Juma’a.” Inji Yero.

Mai magana da yawun gwamna Yero, Yakubu Lere ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN, cewa ana tuhumar Ramalan Yero ne kan zargin wai ya handame naira miliyan 700, wani kaso na kudin kamfen a 2015.

” Kwarai Ramalan ya tabbatar da karbar wannan kudi, miliyan 700, sai dai kuma tun a wancan lokaci, an aiko masa da wadannan kudi ne tare da umarnin abinda zai yi da su. Kuma hakan yayi.

” Baku ga ya fito yana dariya daga ofishin hukumar ba. Abinda ake tuhumar sa akai shine wai mai yasa ya ajiye kudin a ofishin sakataren gwamnatin jiha na wancan lokaci.”

Share.

game da Author