Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Akwa Ibom Dominic Ukpong ya gargadi ma’aikatan jinyar da ke yajin aiki a Jihar cewa sune za su dorawa alhakin duk ran da aka rasa a sanadiyyar wannan yajin aiki da suke yi.
Ukpong yace ma’aikatan jinya dake jihar basu da dalilin shiga wannan yajin aikin da JOHESU ke yi musamman ganin yadda gwamnati ke iya kokarinta wajen ganin ta inganta albashin su,da alawus, alawus din na su a Jihar.
” A saboda haka na ke kira ga mayan ma’aikatan jinya da ke jihar da su janye yajin aikin da suke yi su dawo su fara kula da marasa lafiyar dake asibitocin jihar domin rage yawan mace-macen da ake ta samu a dalilin wannan yajin aiki.
A karshe Ukpong ya bayyana cewa marasa lafiya za su iya samun kula kyauta daga ma’aikatan kiwon lafiya da ke yawo a cikin motocin daukan marasa lafiya zuwa asibiti.
” Sai dai idan har aka kawo mara lafiya asibiti saboda tsananin ciwo dole ne zai biya kudin asibiti.”