Fadan shugaban kasa ta mayar wa kungiyar ‘Amnesty International’ martani kan zargin tauye wa ‘yan gudun hijira da suka yi fama da hare-haren Boko Haram hakkunan su da sojojin Najeriya ke yi.
Armnesty na zargin sojojin da saduwa da mazauna sansanonin ‘yan gudun hijra da karfin tsiya da muzguna musa sau dayawa bayan fitinar da suka sha daga Boko Haram.
Garba Shehu ya yi wannan bayani ne garin a Abuja inda ya kara da cewa rahotannin da ‘Amnesty International’ ta fitar kan sojin Najeriya duk tatsuniya ce kawai, amma babu gaskiya a kai.
” Tabas rahotan ya nuna cewa jami’an tsaro sun muzguna wa wadannan ‘yan gudun hijira amma rahoton bai ce ga sojan da yayi kaza ba ko kuma ga irin abin da yayi.
” Rashin samun wadannan bayanai zai sa binciken da za a gudanar ya zama kamar shirme.”
Bayan haka Shehu yace wannan rahotan na kama da wanda ‘Amnesty International’ ta rubuta tsakanin shekarun 2015 zuwa 2017 sannan ya kuma kara da cewa domin kawar da samun mai-maicin irin haka ne ya sa sojin Najeriya ta kafa tsaurara matakai domin hukunta duk sojan da aka kama da laifin aikata haka.
Sannan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa gwamnatin Amurka cewa gwamnatin sa baza ta amince da tauye wa wani ko wasu hakkunan su ba.
A karshe Sojin Najeriya ba ta amincewa da rahotan ba sannan ta zargi ‘Amnesty International’ da kokarin bata mata suna a idanun duniya.