Abu kamar mai yiwuwa, yau dai ya zama tarihi a majalisar wakilai, domin kuwa sun yi watsi da kudirin kafa Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya, ‘Peace Corps’ da ada suke shirin rattaba wa hannu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki sa ka hannu akan kudirin da suka amnce da ita.
Idan ba a manta ba majalisar kasa ta amince da kafa wannan runduna, amma shugaban kasa ya ki amincewa da saka wa kudirin hannu ta zama doka yana mai cewa Najeriya bata da kudin da za ta iya zuba wa wannan runduna.
A yau dai majalisar tarayya ta ki amincewa ta rattaba wa kudirin hannu a zauren ta yau, ta yi watsi da wannan kudiri kwata-kwata.
Ta yi watsi da kudirin.