An cafke matar da ta sace ‘yar wata a kasuwa

0

Rundunar ‘yan sandar jihar Legas ta gurfanar da matar da ta sace ‘yar shekara biyu a kasuwar doya dake Mile 12 Ketu a jihar Legas.

Kakakin rundunar Chike Oti ne ya sanar da haka wa manema labarai, sannan ya ce sun ceto wannan yarinya ne daga hannun barauniyar mai suna Elizabeth Ibezim a tashar shiga mota dake Ketu.

” Elizabeth ta sace wannan yariya daga mahaifiyar ta ne bata sani ba a wajen sana’ar ta.

” Mahaifiyar yariyar ta sa ihu a lokacin da ta kula cewa ‘yarta bata tare da ita sannan mutane suka taru suka tayata neman ta.”

Oti yace mutanen wannan tasha sun kusa kashe Elizabeth a lokacin da ita mahaifiyar ‘yar ta hango tana kokarin shiga mota tare da yar ta sannan yayi kira ga iyaye su mai da hankali wajen sa ido ga ‘ya’yan su.

Share.

game da Author