Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta ware naira miliyan 165 daga cikin kasafin kudin shekaran 2019 domin siyo dabaru da magungunar kaiyade iyali.
Bayanani sun nuna cewa a shekarar bara gwamnatin ta ware naira miliyan 100 sannan a bana ta ware naira miliyan 75 duk daga cikin kasafin kudin jihar domin haka.
Jami’ar hukumar kula da bada tazarar iyali na jihar Kaduna Nafisa Musa ce ta bayyana haka ranar Laraba a taron wayar da kan masu ruwa da tsaki a jihar game da amfanin da dabarun bada tazarar iyali.
An yi wannan taro ne a Kaduna wanda kungiyar ‘Urban Reproductive Health Initiative (NURHI 2)’ ta shirya.
Nafisa ta bayyana cewa sakamakon da kungiyoyin kiwon lafiya suka samar game ta amfani da dabarun tazarar iyali ya nuna cewa dabarun za su taimaka wurin ceto akalla kashi 30 bisa 100 na rayukan mata da jarirai da ke mutuwa a wannan yanki namu na nahiyar Afrika.
” Amfani da dabarun tazaran iyali zai taimaka wurin gina garkuwar jikin mace sannan idan ta dauki ciki bayan ta huta hakan zai taimaka mata wurin haifo jariri mai koshin lafiya.”
A karshe jami’in NURHI Kabir Abdullahi ya yi kira ga mata wadanda suka kai shekarun haihuwa da su nemi dabarun tazaran haihuwa a asibitocin gwamnati domin ceto rayukan su da na ‘ya’yan su.