Lawali Ali da aka fi sani da Bulaus Udawa ya bayyana wa PREMIUM TIMES yadda wasu masu garkuwa da mutane suka sace shi a titin Kaduna zuwa Birnin Gwari tare da wasu mutane sama da 30 a safiyar Laraba.
” Mun kai mu 30 da masu garkuwa suka tarkata a wannan rana.”
Ya ce a ranar Laraba da misalin karfe bakwai na safe ya shiga motar Kaduna daga Birnin Gwari inda basu kai ko ina ba da tafiya sai suka hango wata babbar motar ta tare hanyar a daidai kauyen Labi. Kafin direban mu ya ankara wadannan mutane sun yo kan m da gudu.
” Nan da nan sai aka fitar da mu daga cikin mota suka kora mu muka nufi cikin wani kungurmin daji tare da wasu mutane da suka kwaso daga wata motar.
” Mun yi awa biyu muna tafiya a cikin wannan daji kafin muka kai mabuyar masu garkuwar.
Lawali ya ce basu muzguna masa ba a lokacin da yake hannun su amma sun kwace duk wasu kaya masu daraja da amfani dake hannun su.
” Bayan sun kammala yi mana tambayoyi sai aka hadani da wasu mutane guda takwas suka ce mu tafi gida abin mu.”
“Mun tafi mun baro sauran mutane 21 tare da su a can cikin dajin.”
Bayan haka wani shugaban karamar hukumar Birnin Gwari wanda baya so a fadi sunan sa da shugaban kungiyar motocin haya dake garin Danladi Duniya sun tabbatar da hakan inda suka bayyana cewa tun daga ranar Talata zuwa Laraba ne masu sace mutane ke aikata wannan mummunar aiki a hanyar garin.