Kotu a jihar Kano ta bada belin tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau da Aminu Wali, bayan hukumar EFCC ta gurfanar dasu a dalilin hannu da ake zargin suna dashi wajen handame wani kaso daga cikin kudin kasa da ake ce wai tsohuwar ministan mai Dezani ce ta basu a lokacin kamfen din 2015.
Ko da yake sai da aka dan yi bata kashi tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da jami’an tsaro a ofishin hukumar dake Kano kafin su samu ya iya shiga ofishin hukumar jiya, a yau Alhamis ne aka gurfanar dasu gaban alkali inda kotu ta ba da belin su.
Ana tuhumar sa da amsar wasu kudade daga hannun tsohuwar ministan albarkatun man fetur Diezani Madueke da ya kai naira miliyan 950 a lokacin kamfen din 2015.
Kakakin tsohon gwamna Shekarau, Sule, ya karyata dalilan da aka bada wai sune yasa aka tasa keyar mai gidan sa.
” Wannan zancen kanzon kurege ce kawai, amma dalilin da ya sa EFCC ta tsare Shekarau bai wuce zargin da ake masa wai ya na kushe gwamnatin Buhari, wannan shine kawai.
Discussion about this post