Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau

0

Ko da yake sai da aka dan yi bata kashi tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da jami’an tsaro a ofishin hukumar dake Kano kafin su samu ya iya shiga ofishin hukumar kan ana tuhumar sa da zargin wai ya ja kaya shima a kudaden da aka warwasa 2015.

Har izuwa yanzu da muke kawo muku wannan labari, Shekarau dai na nan tsare a ofishin EFCC dake Kano.

A cewar hukumar, za a gurfanar da Shekara a kotu a Kano kan tuhumar sa da a keyi da amsar wasu kudade daga hannun tsohuwar ministan albarkatun man fetur Diezani Madueke da ya kai naira miliyan 950 a lokacin kamfen din 2015.

Kakakin tsohon gwamna Shekarau, Sule, ya karyata dalilan da aka bada wai sune yasa aka tasa keyar mai gidan sa.

” Wannan zancen kanzon kurege ce kawai, amma dalilin da ya sa EFCC ta tsare Shekarau bai wuce zargin da ake masa wai ya na kushe gwamnatin Buhari, wannan shine kawai.

Share.

game da Author