Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya ajiye aiki

0

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Nuhu Gidado ya mika takardar ajiye aiki.

Nuhu Gidado ya bayyana cewa kwata-kwata baya jin dadin aikin yanzu, a maimakon ya ci gaba, ya fiye masa ya ajiye aikin kawai ya kara gaba.

Ajiye aiki da mataimakin gwamnan Gidado ya yi shine na uku cikin jerin manyan jami’an gwamnatin jihar Bauchi da suka ajiye aiki tun bayan hawan wannan gwamnati.

A watan Disembar 2017, kwamishinan kasafin Kudi na jihar Shehu Ningi yayi irin haka inda kwatsam ya mika takardar ajiye aikin sa.

A watan Maris din wannan shekarar mai ba gwamna shawara kan harkokin saka jari, Samaila Sanusi ya mika tasa takardar. Dukkan su dai sun koka kan rashin jin dadin aiki da suke yi da gwamnan jihar.

Haka kuma a wannan lokaci ne mataimakin kantoman karamar hukumar Tafawa Balewa Munnir Yisin ya ajiye aikin sa shima.

Share.

game da Author