Sarkin Musulmi ya yi tir da malamai da ‘yan jarida masu haddasa kiyayya

0

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, ya yi tir da malaman addini da ‘yan jarida masu neman jefa kasar nan cikin yaki ta hanyar yada zantukan da ka iya tada zaune tsaye.

Abubakar yay i wannan kakkausan gargadi ne a lokacin da ya ke jawabi da wasu al’ummar Sokoto, jami’an tsaro, malaman addini da kuma ‘yan jarida a fadar sa, a lokacin da ya gayyace su shan ruwan azumin Ramadan ranar Litinin da dare.

Sarkin Musulmi ya kawo misali da wani labarin da aka buga, inda wasu Kiristoci ke cewa, “Idan Leah Sharibu ta mutu a hannun Boko Haram, to za a yi yakin addini a kasar nan.”

Ya ce irin wadannan kalamai ne da ke fitowa daga bakin mutanen banza da wofi.

“Ta yaya mai kiran kan sa shugaban addini zai yi wannan furuci? Ai Boko Haram ba su hada kai da musulmi suka sace yarinyar ba.”

Ya tunatar da Kiristoci cewa Boko Haram sun fi kashe Musulmi sama da Kirista, nesa ba kusa ba, kuma tsohon shsugaban kasa, Goodluck Jonathan ma ya tabbatar da haka.

Sultan ya kara da cewa duk wanda ya yi wannan furucin to matsawar Boko Haram suka kashe yarinya, ya kamata a kama shi.

“Saboda idan suka ji an ce za a yi yaki in suka kashe ta, ai za su ma iya kashe ta din domin kawai su haddasa fitina a cikin kasar nan.”

Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan jarida da su rika yada labarai na gaskiya, maimakon karairayi da sharri da husuma da wasu ke yadawa, musammana a soshiyal midiya.

Ya nemi a taya kasar nan da addu’a domin kawo dawwamammen zaman lafiya da kawar da fitintinun kashe-kashe.

Share.

game da Author