Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya baiwa shugaba Muhammadu Buhari amsa game da korafin da yayi cewa wai an wawushe dala biliyan 16 a lokacin mulkin Obasanjo wajen wai samar wa kasa wutan lantarki.
Obasanjo ya bayyana cewa idan har Buhari bai sani ba, hukumar EFCC da kwamitin musamman na majalisar wakilai ta binciki wannan kwangiloli kuma ba a kama shi da laifi ba.
” Idan Buhari da makarraban sa ba su sani ba, Obasanjo ya yi bayani dalla-dalla game da yadda aka gudanar da wadannan kwangiloli a wancan lokaci da yadda aka kashe wadannan kudade. Duk bayanan na nan a shafi na 41, 42, 43 da 44 a littafin sa da ya buga mai suna ‘My Watch’.
” Sannan idan Buhari ma ba zai iya karantawa bane, ina kira ga makarraban sa da su tsamo wannan wuri da akayi bayanin yadda aka gudanar da kwangilar su tattara su bashi ya karanta. Ko kuma a rubuta masa ta harshen da zai fi gane wa a bashi ya karanta.
Kehinde Akinyemi ne ya saka hannu a takardar mai da martanin a madadin Obasanjo.
Discussion about this post