Babban sakatariyar ma’aikatar ilimi na jihar Kwara Mariam Garba ta bayyana cewa ma’aikatarta ta rufe makarantun firamare 40 a jihar.
Mariam ta bayyana haka nea garin Ilori ranar Talata inda ta kara da cewa gwamnatin ta rufe makarantun ne saboda sabawa sharuddan bude makarantu masu zaman kan su a jihar.
” Mun yi haka ne domin mu inganta ilimin da ‘ya’yan mu suke samu a makarantun kudi da suka jihar.”
Makarantun da aka rufe sun hada da makarantar firamare na ‘Graceland’ dake titin Asa Dam, Ilorin, makarantar firamare na ‘Al Bayan’ dake karamar hukumar Ifelodun, makarantar firamare na ‘Solid Foundation’ dake Shonga a karamar hukumar Offa da sauran su.