Shugaban Kungiyar kwadago na Najeriya, Ayuba Wabba ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kwabe gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, kan cewa wai yana zuga sauran gwamnonin kasar nan su kwaikwayi yadda ya kori ma’aikata a Jihar sa suma su to da shi.
Wabba ya fadi haka ne a wata takarda ta musamman domin maida wa gwamna El-Rufai martani game da wannan batu.
Kamar yadda ya fadi, Wabba ya ce dole su fito karara su gaya wa El-Rufai cewa ba burgewa bane abinda yayi a Jihar Kaduna na tsananta wa mutane da yake yi da dakile musu hanyar cin abincin su.
” Duk da haka maimakon ya tsaya nan, ya zaga yana zuga sauran gwamnonin Kasar nan suyi koyi da irin abinda yayi na koran ma’aikata a Jihar sa.
” Muna so El-Rufai ya sani cewa shi ba Allah bane, kuma komai yayi farko zai yi Karshe wata rana.
” Muna nan muna shirya masu zabe, muna Kira ga ‘yan Najeriya, cewa kowa ya kimtsa katin zaben sa.
A Karshe ya kai kukan kungiyar ga shugaba Muhammadu Buhari da sauran gwamnonin cewa kada su biye wa gwamnan. Kuma suma za su sa ido domin korar ma’aikata gaba-gadai, Saba dokar kwadago ne.