FYADE: Kotu ta daure wani direba a kurkuku

0

Rundunar ‘yan sanda na jihar Filato ta gurfanar da wani dareba mai suna Ahamed Talib mai shekaru 35 a kotu kan zargin sa da laifin yin lalata da ‘yar shekara tara 9.

Dan sandan da ya shigar da karan O.C Ocho ya bayyana a kotu cewa kakan yarinyar, Ahamad Isah ne ya kawo karan wannnan mutumi caji ofis.

” Malam Isah ya bayyana cewa Talib ya dane jikarsa ne a cikin dakin sa bayan ya lallabeta da biskit da kudi Naira 200 a ranar 20 ga watan Maris.”

Sanadiyyar haka ta sami rauni a gabanta wanda dole sai da aka kai ta asibiti bayan an gani.

A karshe alkalin kotun Yahaya Mohammed ya ki amincewa da rokon afuwa da Talib ya yi kuma ya yanke masa hukunci zama a kurkuku na tsawon shekaru hudu tare da biyan duk kudaden asibitin da za a bukata domin yarinyar ta sami lafiya.

Share.

game da Author