Shugaban Npdp, wato gungun ‘yan PDP da suka balle suka taimaka wa APC ta kafa gwamnati, karkashin shugaban su Kawu Baraje ne ya bayyana haka a yau.
Sun dade su na korafin maida su saniyar ware da aka yi, su na cewa an ci gari da yaki da su, amma an ba su ganimar kuturun bawa.
Baraje ya bayyana haka a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara a jiya Lahadi, kamar yadda aka gani ya na bayani a gidan talbijin na AIT.
Ya ce wasikar da ya rubuta wa shugabannin APC, ya yi ne domin kauce wa mummunar baraka a cikin APC.
“Jam’iyyar APC ta gayyace mu domin mu zauna mu sasanta ko kuma na ce mu fahimci juna. An kira taron a ranar da wasikar mu ta cika kwanaki bakwai da damkawa a hannun su. Da ya ke da yawun shugabanni da dama mu ke magana, sai muka ce, musu ba za mu iya zaman ba.
“Ni dama tuni na hango cewa za a samu babbar baraka a zaben shugabannin APC da aka gudanar kwanan nan. Da sun yi amfani da wasikar da muka rubuta musu tun da wuri, to da ba za a samu wannan barakar a APC ba.”
“Amma mu a cikin wasikar mu ba mu ce mun bayar da wa’adi ba ga shugabannin APC.”