Hukumar NAFDAC za fara farautar masu fasakwauri

0

Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa za ta fara yin farautar masu yin fasakwaurin da abubuwan da gwamnati ta hana shigowa da su a tashoshin jiragen ruwa da iyakokin kasar nan.

Hukumar ta ce yin haka ya zama dole ganin cewa amfani da wadannan abubuwa da akan shigo da su na yi wa lafiyar mutanen kasar nan illa.

A karshe hukumar ta ce za ta hada hannu da ma’aikatu, Ofishin masu ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, ma’aikatan sufuri, da sauran hukumomi da ofisoshin da hakan ya shafa domin samun nasara a kai.

Share.

game da Author