PDP ta zama gawa a Jihar Kaduna – Uba Sani

0

Mai ba gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkar siyasa, Uba Sani ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta zama gawa a Jihar Kaduna.

Uba ya fadi haka ne a tattaunawar da yayi da manema labarai bayan kammala zaben shugabannin jam’iyyar APC na Jihar.

Ya kara da cewa babu abinda ya rage wa jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna cewa yanzu kam ta zama gawa.

” Jam’iyyar PDP ta mutu murus a Jihar Kaduna duk da dama da muka basu a zaben Kananan hukumomin da akayi a jihar inda har suka ci wasu Kananan hukumomi a jihar.

” Kowa ya ga yadda akayi zaben a wasu jihohin Kasar nan, babu inda jam’iyyar adawa ta ci ko da karamar hukuma daya ne amma a Kaduna saboda adalcin jam’iyyar APC sun sami nasara a wasu Kananan hukumomin.

” Babu abin da za a iya yi don karya APC a Jihar Kaduna, domin gwamna El-Rufai ya zamo zakaran gwajin dafi a Jihar. Aiki yake yi wa talakawa babu kakkautawa. APC ce za ta sake lashe zabe a 2019 ko tantama bani da shi.

Jam’iyyar PDP ta lashe kananan hukumomi 4, APC 14 cikin sakamakon da aka saki zuwa yanzu. Akwai sauran Kananan hukumomi 5 da za a sake zabe.

Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai ya lashi takobin garzaya wa Kotu domin kalubalantar sakamakon zaben Kananan hukumomin da PDP suka ci.

Share.

game da Author