Duk yadda Sarkin Dawa ko Maidawa ko wani maharbin da ya san namun jeji sosai zai tantance tsakanin gatan biri, gwaggon biri, tsula ko dankwatangwame, ba su da wani sunan da ya wuce a kira su biri. Jinsin su daya, dabi’un su daya, rukunin su daya kuma garken su daya duk a cikin jeji daya.
Kafin jam’iyyar APC ta hau mulki, a wurin kamfen an rika yi wa talakawa ci-da-buguzum, ana cewa idan aka kafa gwamnati za a shimfida adalci a dukkan al’amurra na tafiyar da kasar nan.
Da wannan burga ko bara-da-ka aka rika firgita magoya bayan jam’iyyar PDP ana buga wa jam’iyyar tamburan rashin adalci.
Tafiya ba ta yi nisa ba sai APC ta rika rakitar duk wani dan jam’iyyar PDP ta na goyawa a matsayin dan ta.
Babu ruwan APC da kyakkyawar dabi’ar dan PDP. Ta goya wanda ya sato asusun da uwar sa PDP ke adana kudin ta. Dan PDP ya kantsama wa uwar sa PDP rotse a goshi, an bi shi a guje, amma APC ta bude masa gidan ta, ya rufta a ciki, ta maida kofa ta rufe, ta ce ya zama dan ta.
Daga cikin ‘ya’yan PDP akwai wanda ya haura gidan makwauta ta katanka, aka yi masu ‘ihu ku tare, ku tare.’ Ya tsere ya fada gidan APC, ya tsira. Wani ma uwar ta sa PDP ce ta tsine masa, saboda ya bude baki ya tofa wa uwar sa PDP majina a fuska. APC ta ce ba za ta bar shi a kan titi ya na gararamba ba, ta dauke shi ta goya.
Da ire-iren wadannan ‘ya’ya suka yi yawa ne a cikin APC ta samu damar kafa mulki a Najeriya.
Su dai talaka, babu abin da ke gaban su sai albishir din samun canjin da aka yi musu. Amma sun kasa fahimtar cewa APC da PDP kamar riga ce wadda ka saba sanyawa a daidai. Duk ranar da ka saka ta a birkice, babu wanda zai ce maka ba rigar ka ba ce, sai dai ya ce maka a birkice ka sanya rigar. Saboda dai riga daya ce, ko launi ba ka canja mata ba.
Duk inda ake maganar rashin adalcin da aka rika zargin an yi a zamanin PDP wajen zaben shugabannin jam’iyya, to an yi kamar sa ko ma fiye da shi yanzu a zamanin APC.
Zaben shugabannin mazabu, kananan hukumomi da kuma jiha na jam’iyyar APC da aka gudanar ya tabbatar da cewa APC ta raba hanya da kalmar adalci. Idan an rika sukar PDP da rashin adalci, to a yau APC ita ce ma tushen rashin adalci.
Cikin jihohi 36 har da Abuja, da wahala ka ji inda aka yi zabuka lami lafiya. Ko dai an yi kashe-kashe, ko kone-kone, ko doke-doke, ko kuma a tafka magudin da kai da ji kasan maganar adalci a cikin jam’iyyar ya zama tatsuniya kawai.
A inda rashin kunya ya fi katutu kuwa, kiri-kiri za a dauko wadanda ba su ma tsaya takara ba, a ce su ne suka ci zabe. Saboda lalacewa har ta kai a cikin jam’iyya mai adalci ana zuwa da ‘yan ku-kashe-a-biya ku wurin zabe.
Wasu jihohin da ba a ji hayaniyar komai ba kuwa, to gwamnonin jihohin ne suka yi tuwo-na-mai-na, irin dai yadda aka rika cewa PDP ta yi, kuma aka yi wa talakawa alkawari da rantsuwa cewa abin da za a gyara kenan.
Duk zaben da aka yi cikin rashin adalci da karfa-karfa, kumbiya-kumbiya, magudi da zalunci, ba zai taba haifar da alheri ga talakawan da ke jira su samu sassaucin da aka ce musu za a samar musu ba.
Abin kunya ne a ce zaben shugabannin APC ya karkare kamar yadda ta kasance a jihohin fadin kasar nan.
Talakawa sun shafe shekaru biyar su na hakilon ganin samun canji, amma masu neman shugabanci ido-rufe, ko da tsiya, ko a ci ko a mutu sun maida dimokradiyya na ta tsalle wuri daya kawai.
A yau kowane kauye,kowace ruga da karkara, shiyya, yanki, unguwa, gari, birni da jiha an tabbatar da rashin adalcin da aka tafka a zabukan shugabannin mazabu har zuwa na jihohi.
Shin da wace fuska kuma APC za ta rika kallon jama’a ta na bugun kirji da tinkahon adalci?
Duk wani mai kishin da ya sha wahala da gaganiyar bayar da gudummawa har APC ta kafa mulki, zai ciji yatsa idan har ya fito takarar mukami ya samu kan sa cikin wannan yanayi.
Kai ko wanda bai fito takara ba, idan ya zabi wanda aka yi wa magudi tabbas zai tuna yadda suka rika zagin PDP a shekarun baya. A yanzu zai yi tagumi ya ce ashe “tukururu da bako duk Ambutawa ne.”
To a yanzu da yawan wadanda suka bayar da gudummawar nasarar APC sun a fitowa sun a nuna kura-kurai. Maimakon a fahimce su, sai wasu ‘yan barababiyar siyasa su rika muzanta su. Saboda idon su ya rufe har sun manta da gudummawar da masu korafin suka bayar a baya a lokacin da ake neman mulki.
Duk ginin da aka gina a kan turaku da tubali na rashin adalci, ba ingantacce ba ne, an dai yi ginin da da tubali, amma fa tubalin toka.
A haka za mu shiga zaben 2019 din?
Discussion about this post