PDP sun yi mana magudi a zaben Kananan Hukumomi 4 da suka ci, za mu Kotu – Inji El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP ta yi musu magudi a zaben kananan hukumomi da akayi a jihar makonni biyu da suka wuce.

El-Rufai ya ce jam’iyyar APC ba za ta bari ayi mata murdiya sannan ta sa Ido ta yi shiru ba.

” Yanzu haka mun ci kananan hukumomi 14 saura biyar. Suma din muna so ne mu cin ye su. Saboda haka za mu kotu domin mun tabbatar PDP sun tafka magudi ne a inda suka ci zabe.

” Mun Kashe kudi domin mu inganta zaben amma kuma da yake ba su saba da adalci ba, komai nasu cuta ce sai da PDP ta saka ta zalunci APC a zaben.

” Za a sake zabukka a kananan hukumomi 4 kuma zamu cinye su.

Suma Jam’iyyar PDP sun ce basu yarda da zabukkan ba kuma za su garzaya kotu domin abi musu hakkin su.

El-Rufai ya yaba wa ‘ya’yan jam’iyyar kan yadda kowa ya jajirce aka samu nasara a zaben kananan hukumomin.

Share.

game da Author