Hukumar kwastam ta kasa (NCS) ta sanar cewa za ta raba wa sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar Barno kayan abinci da tufafin da ta kwato a iyakokin kasar nan.
Jami’in hukumar Mohammed Uba ya sanar da haka ranar Laraba inda ya kara da cewa za su kwaso wadannan kaya ne daga ma’ajiyar su dake Legas.
Ya ce shugaban hukumar Hameed Ibrahim Ali ne ya amince da haka a matsayin sa na shugaban kwamitin ‘yan gudun hijira wanda shugaban kasa ya kafa sannan za a raba kayan ne bayan an kammala shari’a akan kayan a kotu.
‘‘Kayan da za a raba sun hada da buhunan shinkafa 25,318, jarkokin man gyada 3,366, galoli 175 na man gyada, balli 1,564 na gwajo da buhuna 196 na takalma.
A karshe Uba y ace hukumar ta kama motoci 30, buhunan shinkafa 5,516, katan 1078 na naman kaza, jarkoki 216 na man gyada, balli 173 na kayan gwanjo, tayoyin mota na gwanjo 683, buhuna 8 na tabar wiwi da kwantena biyu cike da kaya wanda zai kai na naira miliyan 25 da sauran su.
Ya ce za su ajiye wadannan kaya a ma’ajiyar gwamnati har sai gwamnati ta dauki mataki a kan su.
Discussion about this post