Ba za ni ba ‘yan Najeriya kunya ba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai bai wa ‘yan Najeriya kunya ba, ya na mai cewa ana yin duk abin da ya wajaba a yi domin kawar da radadin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi ne.

Haka Buhari ya bayyana a wurin taron gangamin magoya bayan APC jiya Dutse, babban birnin Jigawa, jim kadan kafin ya baro garin.

Ya ci gaba da cewa ya na sane da irin halin kuncin rayuwa da jama’a ke ciki, sanadiyyar matsin tattalin arziki musamman tashi da hauhawar farashin kayan masarufi.

Daga nan sai ya ce gwamnatin tarayya ta hana shigo da shinkafa ne domin ta karfafa wa manoman kasar ta noman shinkafa tare da wadatar da abinci a cikin gida, maimakon dogaro da kasashen waje.

Ya kuma gode wa gwamnati da al’ummar jihar Jigawa dangane da irin karimcin da suka nuna masa a kwanan da ya yi a ziyarar da ya kai jihar.

Da ya jawabi, Gwamnan Jihar, Badaru Abubakar, ya tunatar da jama’a cewa Buhari na bakin kokarin sa, domin ya samu tattalin arzikin kasar nan a durkushe a lokacin da ya hau shugabanci.

Ya ce jihar sa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan raya jiha domin kara samar da sauki da walwalar samun ababen more rayuwa ga daukacin jama’ar jihar.

Cikin abubuwan da gwamnan ya shigo da su, har da wani shiri na kudin akwatu, inda ake raba wa mazabu daga naira dubu 50 zuwa dubu 100,000 a kowane wata.

Share.

game da Author