Buhari ya amince da tallafin naira biliyan 10 ga wadanda rikice-rikicen yankunan karkara ya shafa

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince gwamnatin tarayya ta ware naira bilyan 10 domin bayarwa a matsayin tallafin farfado da wadanda rikice-eikice ya ritsa da su.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Benuwai.

Yankunan karkara da dama a kauyukan Benuwai, Taraba, Zamfara da Kuduna sun afka cikin kashe-kashe da kone-konen rayuka, gidaje da dabbobi, sanadiyyar rikicin makiyaya da manoma da kuma hare-haren ta’addancin fashi da farmaki.

Kakakin mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande, ya bayyana haka a cikin wasu sakonni da ya rika fitarwa a shafin sa na tweeter, ya ce mataimakin shugaban kasar ya samu tarbar Gwamna Samuel Ortom, Ministan Ayyyukan Noma, Audu ogbeh da kuma Darakta Janar na Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA), da wasu jami’ai da dama.

Share.

game da Author