Ko ‘yan sabuwar PDP sun fice daga APC, Buhari zai ci zabe a 2019 – Inji El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba shi da fargaban ko ‘yan sabuwar PDP da suka mara wa Buhari baya a 2015 sun fice daga jam’iyyar APC, Buhari zai ci zabe ba hamayya.

El-Rufai ya fadi haka ne a fadar shugaban Kasa bayan ganawa da yayi da shugaba Muhammadu Buhari.

” Jihohin da ake cewa jiga-jigan sabuwar PDP din sun ba da gudunmuwa ai bai wuce jihohin Kwara, Sokoto, Kano da Adamawa ba. Ban tsammanin akwai Ribas a ciki. Kuma idan ka duba yadda zaben Buhari ke kasancewa a wadannan jihohi kai ma kasan Buhari ba sa’an su bane.

” Buhari ya doke Shekarau a 2007 duk da yana gwamnan jihar Kano amma shi ya ja kuri’un Kano. Haka Buhari zai sake cin Kwara, Adamawa da sauran jihohin da suke ta korafi a akai.

” Maganar Kano kuwa ai a baje take, Kano ta Buhari ce kowa ya sani babu tantama a kai. Kowa ya ga irin miliyoyin mutanen da suka yi masa lale-lale marhaban da ya ziyarci Kano. Kuma ai ba da kwankwaso ya tafi Kanon ba. Kano tabbas ta Buhari ce.

A nawa ganin sun rubuta wasikar su da korafe-korafen su, za a duba.

Idan ba a manta ‘yan kungiyar sabuwar PDP na wancan lokaci sun rubuta wa jam’iyyar APC wasika cewa ana nuna musu wariya da danniya a jam’iyyar inda gwamnati mai ci ta wancakalar da su kamar basu bada gudunmuwa ba a zaben 2015.

Bayan haka El-Rufai ya fadi cewa ya gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 4 wajen shirya zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Kaduna, sannan ya yi kira ga gwamnatin sauran jihohi da su gwada yin amfani da naurar zabe da akayi amfani da su a zaben Kaduna.

Share.

game da Author