Wasu malaman addinin musulunci da na Kirista sun gargadi ma’iakatan jinya da ke yajin aiki da su nesan ta kasu daga maganar karbar albashin da basu yi aiki a kai ba.
Farfesa Abdulrasaq Abubakre da Cornelius Fawenu sun kwabi su da su janye yajin aiki idan har suna so su ci albashin su hankali kwance.
Malaman sun bayyana cewa addinan da muke bi guda biyu wato Musulunci da na kiristanci sun yi hani da cin albashin da ba ayi wa aiki ba.
Malaman sun yi wannan kira ne a garin Ilori, jihar Kwara sannan sun nuna rashin jin dadin su ga irin bukatun da kungiyar JOHESU ke nema gwamnati ta biya musu cewa wasu daga ciki bai kamata su neme su ba daga gwamnati.
” Ku fa tuna biyan zakka da albashi ko kudin da ba kuyi wahalar samun su ba, ba za ku sami ladar da ake samu idan anyi ba.
” Kamata ya yi ma’aikatan jinya su fahimci cewa ceto rayukan mutane ya na da alfanu so sai har ga Allah.
A karshe sun kuma hori ma’aikatan da su daina hada kan su da Likitoci, ko kuma neman a biya su albashi iri daya da likitocin kasar nan.