Rundunar ‘yan sandar jihar Gombe ta gurfanar da wani magidanci mai shekaru 50 a kotun dake karamar hukumar Yamaltu/Deba kan zargin sa da akeyi na dirka wa ‘yar cikin sa ciki.
Dan sandan da ya shigar da karar Baba Shekari ya bayyana cewa Samaila Zakari ya aikata haka ne a ranakun 2 da 8 ga watan Mayu a gidan sa dake garin Deba a karamar hukumar Yamaltu/Deba.
” Binciken da muka yi ya nuna cewa a kowani dare na wadannan ranaku da misalin karfe 10 Zakari kan danne ‘yar tasa inda yake yin lalata da ita.
” Sanadiyyar haka wannan yarinya ta samu juna biyu, wato tana dauke da cikin mahaifin ta.”
Ko da yake Zakari ya musanta aikata haka amma dan sanda shekari ya roki kotun da ta daga shari’ar zuwa wani lokaci domin ba ‘yan sanda damar kammala bincike akai.
Kotu ta daga shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Mayu sannan ta yanke hukunci daure Zakari a kurkuku har sai an kammala shari’ar.