Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan da suka sa aka hambarar da shi daga kan mulki, a lokacin da ya ke shugabanci na mulkin soja, har aka kulle shi a cikin gida tsawon shekara uku.
Ya ce hambarar da shi da aka yi a lokacin wato cin hanci da rashawa ne suka yi galaba a kan mulkin sa.
Buhari ya na magana ne a wurin bude sabuwar hedikwatar ofishin EFCC da aka gina, kusa da hedikwatar Budadddiyar Jami’ar Najeriya, NOUN, a Abuja.
Ya ce amma duk da haka, guyawun sa ba su sanyi ba da ake cewa idan ka na fada da cinn hanci, to cin hanci zai juyo ya far maka da irin na sa haukan fadan.
“A karon farko da na fito ina fada da cin hanci, sai cin hanci ya juyo ya na fada da ni. Aka hambarar da ni, aka kuma kulle ni har tsawon shekaru uku.”
Daga nan sai ya ce dawowar da ya yi neman shugabanci har ya samu nasara a 2015, ya yi ne da kyakkyawan kudiri da niyyar yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.
Buhari ya jinjina wa kan sa da kan sa daga kokarin da ya ce ya yi na kwato nairori tiriliyan ba daya ba daga hannun wadanda suka wawure dukiyar kasar nan.
Daga nan ya ci gaba da cewa ko badade, ko bajima sai an hukunta wadanda suka wawure dukiyar kasar nan.
Dangane da zargin gwamnatin sa na yi wa wasu bi-ta-da-kulli ne kawai da kuma nuna son kai wajen ganin damar kyale wasu ana bincikar wasu wajen yaki da cin hanci, Buhari ya ce duk abin da gwamnatin sa za ta yi to ta na yi ne a bisa tsarin da doka ta gindaya.
Daga nan sai ya yi kira ga majalisar tarayya ta kara kaimi wajen sake nazarin dukkan wasu nakasu da dokar Najeriya ke tattare da su masu kawo wa shari’a cikas.
Gwamnati ta kara kula da jami’an EFCC, Inji Yakubu Dogara
A na sa jawabin, Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya yi kira da a kara wa jami’an EFCC albashi da alawus-alawus, wanda zai zama kariya a gare su, domin gudun kada yawun su ya rika gudawa idan aka sinsina musu kudade da niyyar ba su toshiyar baki.
Dogara ya ci gaba da cewa gina katafariyar hedikwata ta EFCC ba shi ne babban abin birgewa ko tinkaho wajen yaki da cin hanci da rashawa ba.
Ya ce kula da ma’aikata shi ne mafi a’ala.
Wannan kalami na Dogara ya zaburar da ma’aikatan EFCC, har suka rika tafa masa da karfi, raf-raf-raf, su na cike da murna kan wannan furuci da kira da ya yi.
Daga nan kuma sai ya ce akwai babban aiki wanda ya wajaba a yi, domin ana yi wa duk dan Najeriya kallon maras gaskiya.
Sai Dogara ya ce akwai bukatar a nuna wa jama’a fa cewa a Najeriya akwai mutane miliyoyi da ba su yarda a hada kai da su a yi sata ko a wawuri dukiyar kasa ba.
Magu ya yaba wa shugabannin EFCC da aka yi kafin shi
Da ya ke jawabi, Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya ce a cikin shekaru biyu da rabi da ya yi a kan shugabancin hukumar EFCC ta gurfanar da mutane 486. Cikin 2018 kadai ta gurfanar da mutane 89, wanda a karon farko aka samu wannan adadin a cikin watanni shida na farkon shekara.
Daga nan ya kara da cewa hukumar ta karbo kudaden gwamnatin tarayya har naira biliyan 500, kuma duk gwamati na sane da kudaden.
Daga nan ya jinjina wa shugabannin EFCC da suka gabace shi, musamman Nuhu Ribadu, wanda ya fara samar wa hukumar ofishin ta na farko a Wuse, Abuja.
Ya ce bukatar wannan babba kuma hedikwata ta dindindin da aka bude a yau Talata, ya zama wajibi saboda karuwar aiki da ke tasowa a koda yaushe, da kuma batu na tsaro, sai kuma dalilai na boyewa da adana sirri.