Majalisa ta gayyaci Sanata Ndume da Omo-Agege kan zargin su da hannu a sace sandar mulki

0

Kwamitin Binciken Satar Sandar Mulki a Majalisar Dattawa, ya gayyaci Sanata Ali Ndume da Omo-Agege da hannu wajen sace sandar mulki da aka yi kwanakin baya a majalisar Dattawa.

Shugaban Kwamitin Bincike, Sanata Bala Ibn Na’Allah ne ya bayyana sanarwar gayyatar sanatocin biyu a yau Talata, a Abuja.

Gayyatar da aka yi musu ta biyo bayan wasu shaidu ne daga shugabannin bangarorin jami’an tsaron da ke kula da Majalisar Tarayya.

SSS da ‘yan sanda sun yi zargin cewa Sanata Omo-Agege ne ya shiga da zugar ‘yan daba girda-girdan karti majiya karfi su bakwai, inda suka rikita zaman majalisar, har daya ya sungumi sandar mulki suka gudu da ita.

An dai tsinto ta daga baya, a karkashin wata gada, kan hanyarc fita daga Abuja, daidai kusa da City Gate, hanyar Gwagwalada.

An kuma yi zargin cewa Sanata Ndume ne ya kawo wa mai tsaron sandar mulki cikas, har ya kasa dauke ta ya boye, abin da hakan ya bai wa kartin samun damar sungumar ta suka arce da ita.

Share.

game da Author