Ma’aikatan jinya na asibitocin jihar Bauchi sun bi sahun yajin aiki gamagari na ‘JOHESU’

0

A ranar litinin ne ma’aikatan jinya na jihar Bauchi suka bi sahun ‘yan uwan su dake karkashin inuwar kungiyar JOHESU yajin aikin gama gari da ta fara a kasar nan.

Kamfanin Dallancin Labaran Najeriya ce ta ruwaito haka sannan ta bayyana cewa ya tsaya cak a asibitocin gwamnati dake jihar.

Shugaban kungiyar reshen jihar Bauchi Ibrahim Maikudi ya bayyana wa NAN cewa tun a makon da ta gabata ne suka so su bi sahun ‘yan uwan su don shiga yajin aikin amma hakam bai yiwu ba sai yanzu.

A karshe shugaban asibitin ‘Specialist Hospital’ dake Bauchi Ya’u Sulaiman yace a dalilin yajin aikin dole sai da asibitin ta sallami wasu daga cikin marasa lafiya domin rage cinkoso.

Share.

game da Author